..Daga Bakin Mai Ita tare da Hadiza Musa Maikano
A wannan makon muna kawo muku tattaunawa da mawaƙiyar masana'antar fina-fina-finai ta Kannywood, Hadiza Musa Mai Kano.
An haifi Hadiza a birnin Kano inda kuma ta yi karatunta a jihar Adamawa sannan ta sake komawa Kano ta fara harkar waƙe-waƙe kafin ta yi aure.
Mawaƙiyar tana da yara uku amma a yanzu haka ba ta da aure.
Hadiza ta ce kallon ƴan wasan Hausa da ta je yi a Sabon Titi a Kano ne ya fara saka mata sha'awar shiga harkokin fina-finai.
"Ina yin waƙoƙin fina-finai da na siyasa da na tallace-tallace," in ji Hadiza Musa.
Mawaƙiyar wanda ta ce ta shafe shekaru fiye da 20 a Kannywood, ta ce ta yi waƙoƙi da dama ciki har da Jamila ta Iya Ɗaura Zane da Jarida da Zabari da Gambiza da Man Taiga da Ranar Murna da Guɗa da dai sauran su.
"Babu abin da waƙa ba ta yi min ba. Na je Makka da waƙa. Na sayi gida da waƙa. Na sayi motoci da waƙa. Kai ko lokacin aurena sai kawai cewa na yi na gama komai domin na sayi duk abin da ake buƙata. Alhamdu lillah babu abin da zan ce da waƙa." In ji Hadiza.



