Halin da katafariyar kasuwar Taminas ke ciki shekara 20 bayan konewarta
Halin da katafariyar kasuwar Taminas ke ciki shekara 20 bayan konewarta
A shekarar 2022 ne katafariyar kasuwar Taminas da ke birnin Jos na jihar Filato ke cika shekara ashirin da konewa.
Gobarar da ta tashi a farkon shekara ta 2002 ta durƙusar da kasuwar wacce dubban daruruwan 'yan kasuwa ke neman abinci daga cikinta.
Tana ƙoƙarin farfaɗowa ne kuma, sai aka sake samun tagwayen bama-bamai a 2014 inda suka sake tsugunnar da Taminas.
Gwamnatoci daban-daban sunyi alkawarin sake gina kasuwar, amma har yanzu ba'a kai ga ginata ba.
A wannan bidiyon BBC ta tattauna da wasu 'yan kasuwa da suka tafka mummunar asara a lokacin gobarar.



