Abubuwan da ake sa ran Kim Jong-un zai aiwatar a 2023

Kim Jong-un

Asalin hoton, REUTERS/KCNA

    • Marubuci, By Jean Mackenzie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC a Seoul

Koriya ta arewa ta yi abubuwan da suka kafa tarihi a 2022.

Ta harba makamai a shekarar 2022, masu yawan da ba ta taɓa yi ba a baya.

Kashi ɗaya cikin huɗu na munanan makaman roka da ƙasar ta harba sun faru ne a 2022.

Kuma a shekarar ne Kim Jong-un ya bayyana cewa Koriya ta Arewa ta shiga jerin ƙasashen da suka mallaki makaman nukiliya.

Wannan ya haifar da fargaba mafi muni a yankin tun bayan 2017, lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar dirar wa Koriya ta Arewa.

Me zai faru a nan gaba?

Bayani kan gwajin makamai da Koriya ta Arewa ta yi

Ci gaba da bunƙasa makaman nukiliya

A shekarar 2022, Koriya ta Arewa ta samu bunƙasa a shirinta na makaman nukiliya.

A shekarar 2022, ƙasar ta fara ne da gwajin makamai masu ƙaramin zango waɗanda aka tsara cewa za su iya kai wa Koriya ta Kudu.

Sai kuma makamai masu cin matsakaicin zango, waɗanda za a iya amfani da su wurin kai wa Japan hari.

Ya zuwa ƙarshen 2022, ƙasar ta samu nasarar gwajin makaminta mafi ƙarfi, Hwasong 17, wanda bayanai suka ce zai iya kaiwa ko ina a Amurka.

Yayin da shekarar ta kusa ƙarewa, shugaban ƙasar ya tara shugabannin jam'iyya mai mulki domin samar da manufofin da ya ke son cimmawa a 2023.

Babban ƙudurinsa na 2023 shi ne haɓɓaka samar da makaman nukiliya cikin hanzari.

Ya ce hakan zai haɗa da haɗa ƙananan makaman nukiliya waɗanda za a iya amfani da su wajen yaƙar Koriya ta Kudu.

...

Asalin hoton, KCNA

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Domin samar da makaman nukiliya na yaƙi, wajibi ne Koriya ta Arewa ta ƙera ƙaramin makamin wanda za a iya ɗarowa a kan ƙananan rokoki.

Sai dai har yanzu duniya ba ta ga shaidar da ke nuna cewa Koriya ta Arewa ta samu nasarar yin hakan.

An ta sa ran cewa ƙasar za ta yi gwajin makamin a 2022 amma hakan bai faru ba, da yiwuwar ƙasar ta samu nasarar hakan a 2023.

Wasu sauran abubuwan da ke cikin jerin ababen da Kim Jong-un ke son samarwa a sabuwar shekarar su ne tauraron ɗan'adam na leƙen asiri, wanda ya ce za a harba zuwa sararin samaniya a wannan shekarar.

Sai kuma wani makamin roka na ƙasa da ƙasa, wanda za a iya harba shi zuwa Amurka wanda yake da inganci fiye da wanda take da shi a yanzu.

Saboda haka za a iya cewar akwai wasu ayyukan da ƙasar ta fara daga 2022 waɗanda za su shiga shekarar 2023.

Koriya ta Arewar za ta ci gaba da ingantawa da faɗaɗa rumbunta na makaman nukiliya, tare da bijire wa takunkuman Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tuni dai ƙasar ta fara, inda a ƙasar da awa uku bayan shiga sabuwar shekara Koriya ta Arewa ta gudanar da gwajin makaminta mai linzami na farko.

Sai dai wani masani, Ankit Panda ya ce yawancin gwajin nukiliya da Koriya ta Arewa za ta yi a 2023 zai zamo na atisaye ne, kasancewar a yanzu ƙasar na shirye-shiryen yadda za ta yi amfani da makaman nata ne a lokacin faɗa.

Batun tattaunawa

...

Asalin hoton, KCNA

Idan aka dubi jerin abubuwan da Koriya ta Arewar ke shirin cimmawa a 2023, zai yi wahala shugaban ƙasar ya amince ya hau kan teburin shawara da Amurka.

A 2019 ne yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya a yankin Koriya ta wargaje, kuma tun daga wancan lokacin Mr Kim bai sake nuna aniyar yin wata tattaunawar ba.

Ana ganin cewa yana jira ne sai Koriya ta Arewa ta tabbatar wa duniya cewar tana iya yi wa ƙasashen duniya irin su Amurka da Koriya ta Kudu illa kafin ya tattauna da su domin ƙulla kowace irin yarjejeniya.

A maimakon tattaunawa, Koriya ta Arewa ta ci gaba da ƙoƙarin yauƙaƙa dangantakarta da Rasha da kuma China.

Mene ne ke faruwa a cikin ƙasar?

Wata babbar tambaya ita ce shin mene ne al'ummar Koriya ta Arewa ke tsammanin samu a 2023?

Sun kwashe shekara uku suna fuskantar matsananciyar dokar kulle iyakokin ƙasar sanadiyyar korona.

Har dakatar da hada-hadar kasuwanci aka yi domin gudun kada korona ta shiga ƙasar, wadda ƙungiyoyin bayar da agaji suka yi amannar cewa ta haifar da matsanancin ƙarancin abinci da magunguna.

A bara ne shugaban na Koriya ta Arewa ya fito fili ya bayyana cewa ƙasar na fama da ƙarancin abinci.

A watan Mayun 2022 kuma ƙasar ta bayyana cewa cutar korona ta ɓarke a cikinta, sannan daga baya kuma ta ce ta magance cutar.

Shin ko a 2023 ƙasar za ta buɗe iyakokinta da China tare barin kayan masarufi su isa ga al'umma?

Mr Kim da ɗiyarsa a watan Nuwamba, 2022

Asalin hoton, KCNA

Sake buɗe iyakoki da China ta yi labari ne mai daɗi.

Rahotanni na cewa Koriya ta Arewa na yi wa mutanen da ke zaune kan iyaka da China rigakafin korona.

Wani abin da zai ja hankalin mutane kuma shi ne lamurran da za su nuna ko wane ne zai gaji Mr Kim.

Babu wani cikakken bayani kan wanda Kim ke son ya gaje shi, to amma a bara ne a karon farko, ya bayyana ɗaya daga cikin ƴayansa - mace ce mai suna Kim Chu.

Yanzu ana yawan ganin ta a wuraren tarurrukan soji, inda a ranar shigar sabuwar shekara aka fitar da wasu sabbin hotunan nata.

Hakan ta sanya wasu ke raɗe-raɗin cewa ita ce shugaban ya zaɓa.

Ba dai za a iya hasashen abin da zai faru a ƙasar ta Koriya ta Arewa a 2023 ba.