Ku San Malamanku tare da Sheikh Idris Muhammad Muhammad
Ku San Malamanku tare da Sheikh Idris Muhammad Muhammad
Shirin Ku San Malamanku na wannan mako ya tattauna ne da Sheikh Idris Muhammad Muhammad, wanda aka haifa a birnin Lafiyar Barebari a shekarar 1974.
Ya fara karatunsa na firamare a Lafiya, kafin ya tafi zuwa birnin Jos inda ya yi sakandire.
Ya samu damar shiga Jami’ar Al-Azhar a ƙasar Masar lokacin da yake gab da kammala karatun difloma a Jos.
Sheikh Idris Muhammad ya kammala karatun digirinsa na biyu a Jami’ar Jihar Nasarawa, kafin daga bisani ya koma aiki a Jami’ar Tarayya ta Lafiya.
Malamin ya ce a yanzu haka shi ne shugaban tsangayar nazarin Larabci a Jami’ar Tarayya ta Lafiya.



