Ko ina makomar Nijar bayan hamɓarar da Shugaba Bazoum daga mulki?
Ko ina makomar Nijar bayan hamɓarar da Shugaba Bazoum daga mulki?
Tun bayan hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed na Nijar a ranar Laraba 26 ga watan Yuli, ana ci gaba da nuna taraddadi game da makomar ƙasar ta yankin Sahel.
Ƙasar dai na fama da ɗumbin matsalolin tsaro saboda ayyukan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi, sannan kusan duka maƙwabtanta na fama da ƙalubalen taɓarɓarewar tsaro.




