Beijing Olympics: Abu biyar da ya kamata ku sani game da gasar Olympics ta hunturu

Latsa hoton sama ku kalli bidiyon:

A ranar Juma'a ne ake fara wasannin gasar Olympics ta hunturu wato Winter Olympics a birnin Beijing na China.

Za a gudanar da gasar ce yayin da wasu ƙasashe ke kiran da a ƙaurace wa China saboda take haƙƙin ɗan Adam da ake zargin ƙasar da yi, musamman muzguna wa Musulmai 'yan ƙabilar Uyghur.

Ku kalli waɗannan da ma wasu abubuwa huɗu da ya kamata ku sani game da gasar wasanni mafi girma a duniya a wannan shekara.