Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mini Hanya 02/10/2021; Hira da Sarkin Zazzau kan cikarsa shekara daya
Ku latsa sama don sauraron shirin:
A Najeriya, yayinda hukumomin jihohin Arewacin kasar ke daukar matakai don kawo karshen hare-haren yan bindiga, wasu manyan Sarakuna sun koka kan yadda ake sakin wasu batagari da ake zargin su da hannu a sace sacen Jama'a da kuma wasu laifuffuka.
Mai Martaba Sarkin Sarkin Zazzau Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli wanda a cikin makon mai kamawa ne zai cika shekara daya akan karagar sarauta ya ce wajibi ne sai an dukufa wajen gudanar da addu'o'i don shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan
A Filin Gane Mini Hanya na wannan makon, Yusuf Tijjani ya tattauna da sarkin kan batutuwa da dama amma ya fara ne da tambayar Sarkin na Zazzau yadda tafiya ta kasance akan gadon Sarauta a tsawon shekara guda.