Gane Mani Hanya: Abin da na fi jin daɗi shi ne taimaka wa 'yan gudun hijira - Gwamna Zulum

Latsa hoton sama ku saurari hira da Gwamna Babagana Zulum

Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zullum ya shahara a Najeriya sakamakon salon mulkinsa, musamman ma yadda yake yin kasada wajen shiga yankunan jihar da ke fama da rikicin Boko Haram.

Kuma irin wannan jagorancin nasa ya sama masa tagomashi a ciki da wajen jiharsa, har wasu na ganin cewa ya kai a fafata da shi a siyasar ƙasa baki ɗaya.

A filinmu na Gane Mani Hanya, Ibrahim Isa ya tattauna da shi a kan ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban jihar Borno da kuma irin burin da yake da shi a harkar siyasa a Najeriya.