Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gane Mani Hanya: Dalilin da ya sa shugabannin kudu ba sa sukar 'yan IPOB - Rochas
Latsa hoton sama ku saurari cikakkiyar hira da Sanata Rochas Okorocha
A Najeriya, a yau ne ake bikin cika shekara 22 da komawar kasar kan turbar demokuradiyya, inda mahukunta da `yan kasa ke kididdigar nasarori da kuma kalubalen da kasar ke fuskanta.
Sai dai bikin wannan karon ya zo a lokacin da Najeriyar ke fuskantar barazana daga `yan kungiyar IPOB, wato `yan kabilar Igbo masu fafutukar ballewa don kafa kasarsu ta Biafra.
Ana dai zarginsu da kisan mutane da dama, ciki har da jami`an tsaro, da kona ofisoshin `yan sanda da lalata dukiyar jama`a. Mahukunta dai na ikirarin daukar matakai da nufin dakile su.
Amma tsohon gwamnan jihar Imo, kuma dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Rochas Okorocha ya tattauna da Ibrahim Isa a kan wannan batu, kuma ya ce amfani da karfi kadai ba zai magance matsalar ba.