Shirin Mata 100 Na BBC: Ana dukanmu a tilasta mana gwajin budurci a gidan yarin Masar

Ku latsa hoton da ke ƙasa don kallon bidiyon:

A cikin wannan bidiyon da aka yi amfani da zane-zane, wata mace ta bayar da labarin yadda aka yi mata wani gwaji na wulaƙanci da ya hargitsa tunaninta a yayin da take tsare a gidan yari - duk da sunan gwajin budurci.

Duk da cewa babu wani tabbaci na kimiyya kan gwajin, ana yi wa mata irin wannan gwajin a ƙasashe fiye da 20 a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Sashen Larabci na BBC ya zanta da wata tsohuwar fursunar siyasa a Masar, wacce ta bayyana irin halin da ta shiga na muzantawa da aka yi mata gwajin budurci lokacin tana tsare a gidan yari.

Mun sauya sunanta saboda tsaro.

Ga ƙarin labarai masu alaƙa da za ku iya karantawa