Lafiya Zinariya: Amfanin barin tazara tsakanin haihuwa ga lafiyar mace

Bayanan sautiLafiya Zinariya: Abin da ba ku sani ba dangane da barin tazara

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tsarin iyali da barin tazara tsakanin haihuwa hakkin dan Adam ne. Duk mata da miji na da damar daukar matakin ko haihuwa ko barinta a lokacin da suka so.

Hukumar ta ce wannan damar na karfafa wa mata gwiwa kuma tana ceto rayuwarsu ta hanyar rage samun cikin a lokutan da bas u shirya samu ba, da zubar da ciki ta hanyoyi masu cike da hadari.

Haka kuma, Hukumar ta ce tsarin iyali da barin tazara tsakanin haihuwa na inganta rayuwar jarirai da tabbatar da cewa an haifi yara masu koshin lafiya.

A wani bangaren kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mata miliyan 232 ne a duniya suke son barin tazara a tsakanin haihuwa amma saboda rashin cikakken bayani dangane da hanyoyin da ya kamata su bi, da rashin goyon baya daga mazajensu, ba sa iya bin hanyoyin da suka dace a bi don tsarin iyalin.