Lafiya Zinariya: Illolin cutar malaria a kan mata masu ciki
Ku latsa hoton da ke sama don sauraron cikakken shirin wanda maimaici ne:
Hukumar lafiya ta Duniya ta ce, Yammacin Afrika ne ya fi ko ina yawan mata masu juna biyu da suka kamu da cutar malaria, a shekarar 2018.
Kuma Najeriya da jamhuriyyar demokradiyyar Congo, nan ne inda mata masu ciki suka fi kamuwa da cutar zazzabin cizon sauron a nahiyar Afrika baki daya, a wancan shekarar.
Hukumar ta ce yankunan Yammaci da Tsakiyar Afrika sun samu kashi 35 cikin dari na masu ciki da suka kamu da cutar.
Sai yankunan gabashi da Kudancin Afrika da ke biye da su da kashi 20 cikin dari.