Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Yunkurin samar da audugar mata ga 'yan makaranta
Latsa hoton da ke sama don jin cikakken shirin:
Al'umma da kungiyoyin fararen hula na da rawar da za su taka wajen ganin sun taimaka wa 'yan mata 'yan makaranta samun audugar da za su yi amfani da ita a lokacin da suke jinin al'ada.
Rashin samun audugar na jefa 'yan mata cikin hadarin kamuwa da wasu cututtuka, wanda hakan kan shafi lafiyarsu.
Wata kungiya a arewacin Najeriya ta yi bincike kan girman matsalar rashin samun audugar, inda ta ce ta gano wasu abubuwa da dama.