Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Dalilan da ke sa wasu masu jego yunkurin raunata kansu ko jariransu
Latsa hoton da ke sama don sauraron cikakken shirin.
Dokin samun sabon jariri da murna kan sanya a wasu lokuta hankalin dangi ya fi karkata kan jariri, lamarin da ka iya jefa matar da ta haihu cikin hadarin kamuwa da matsananciyar damuwa.
Hakan na daya daga cikin dalilan da likitoci suka bayyana cewa suna janyo matsananciyar damuwa ga masu jego.
Sai dai alkaluma sun nuna cewa yawan mazan da kan fada cikin irin wannan yanayi na matsananciyar damuwa idan an yi musu haihuwa ya haura na mata a fadin duniya.