Ku aiko mana bidiyon girkinku na Ramadana - 2026

A lokacin azumin Ramadana mukan yi girke-girke na musamman domin ɗebe kewa da kuma samar mana sinadaran gina jiki.

Haka nan mukan zauna tare domin shan ruwa da iyalai cikin raha da jin dadi.

Ku sanya bidiyon abincin buɗe-baki na musamman da kuka haɗa wa iyalanku ta yadda wasu za su iya kallo su kwaikwaya.

Za kuma ku iya sanya bidiyon yadda kuka yi buɗe-baki tare da iyalanku a cikin nishaɗi.

Kada bidiyonku ya zarce tsawon minti uku, sannan a ɗauki bidiyon da kyau, domin bidiyon da ba a ɗauka da kyau ba ba zai samu shiga ba.

Our data policy

A yayin da muke muradin karanta dukkanin sakonnin imel din da kuka aiko mana, ba za mu iya ba ku tabbacin aika muku da amsa ba. Akwai yiwuwar mu aika muku amsar imel din ko mu tuntube ku domin karin bayani. Idan da hali, za mu iya gyara bayanan da kuka aiko, mu kuma wallafa a shafukanmu na BBC Hausa. Idan ba kwa son a sanya bayananku, to sai ku gaya mana. Ba za mu bai wa duk wanda ba ɗan BBC bayananku ba tare da izininku ba.

BBC ce babbar mai kula da bayanan da kuka bayar. BBC za ta sarrafa waɗannan bayanan saboda buƙatarta a matsayinta ta kafar yaɗa labarai a matsayin shaida. Idan kuna da tambaya a kan yadda BBC ke adana bayananku, ku duba nan domin ganin Tsarin Sirrin Na BBC: https://www.bbc.co.uk/usingthebbc/privacy/

BBC za ta adana bayananku har sai zuwa lokacin da aka kammala amfani da su.