
Bayanan juyin mulkin da suka yi nasara a Afirka cikin sama da shekara 70
An samu kusan juyin mulki 130 da suka yi nasara, a cikin ƙasashen Afrika 36, tun 1952 lokacin da Sarki Farouk na Masar ya zama shugaban wata ƙasa a Afirka na farko da aka hamɓarar.
Shugabannin da aka hamɓarar
- Shugaban ƙasa
Gabon
Karanta ƙarin bayani... Mohamed Bazoum
Shugaban ƙasaNijar
Karanta ƙarin bayani...Paul-Henri Sandaogo Damiba
Shugaban riƙon ƙwaryaBurkina Faso
Karanta ƙarin bayani...Rocha Kabore
Shugaban ƙasaBurkina Faso
Karanta ƙarin bayani...Abdalla Hamdok
FiraministaSudan
Karanta ƙarin bayani...Alpha Condé
Shugaban ƙasaGuinea
Karanta ƙarin bayani...Bah N'daw
Shugaban ƙasaMali
Karanta ƙarin bayani...Ibrahim Boubacar Keita
Shugaban ƙasaMali
Karanta ƙarin bayani...Omar al-Bashir
Shugaban ƙasaSudan
Karanta ƙarin bayani...Robert Mugabe
Shugaban ƙasaZimbabwe
Karanta ƙarin bayani...Blaise Campaore
Shugaban ƙasaBurkina Faso
Karanta ƙarin bayani...Mohamed Mohamed Morsi
Shugaban ƙasaMasar
Karanta ƙarin bayani...François Bozizé Yangouvonda
Shugaban ƙasaJamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Karanta ƙarin bayani...Amadou Toumani Toure
Shugaban ƙasaMali
Karanta ƙarin bayani...Muammar Gaddafi
Shugaban ƙasaLibya
Karanta ƙarin bayani...Laurent Gbagbo
Shugaban ƙasaIvory Coast
Karanta ƙarin bayani...Hosni Mubarak
Shugaban ƙasaMasar
Karanta ƙarin bayani...Zine el Abidine Ben Ali
Shugaban ƙasaTunisiya
Karanta ƙarin bayani...Mamadou Tandja
Shugaban ƙasaNijar
Karanta ƙarin bayani...Kaftin Moussa Dadis Camara
Shugaban ƙasaGuinea
Karanta ƙarin bayani...Marc Ravalomanana
Shugaban ƙasaMadagascar
Karanta ƙarin bayani...Aboubacar Somparé
Shugaban ƙasaGuinea
Karanta ƙarin bayani...Sidi Ould Cheikh Abdallahi
Shugaban ƙasaMurtaniya
Karanta ƙarin bayani...Maaouya Ould Sid' Ahmed Taya
Shugaban ƙasaMurtaniya
Karanta ƙarin bayanai...Fradique de Menezez
Shugaban ƙasaSao Tome da Principe
Karanta ƙarin bayani...Ange-Felix Patasse
Shugaban ƙasaJamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Karanta ƙarin bayani...Henri Konan Bédié
Shugaban ƙasaIvory Coast
Karanta ƙarin bayani...Joao Bernardo Vieira
Shugaban ƙasaGuinea-Bissau
Karanta ƙarin labarai...Tadjidine Ben Said Massonde
Shugaban ƙasaKomoros
Karanta ƙarin bayani...Ibrahim Bare Mainassara
Shugaban ƙasaNijar
Karanta ƙarin bayani...Johnny Paul Koroma
Shugaban ƙasaSaliyo
Karanta ƙarin bayani...Pascal Lissouba
Shugaban ƙasaKongo
Karanta ƙarin bayani...Ahmad Tejan Kabbah
Shugaban ƙasaSaliyo
Karanta ƙarin bayani...Mobutu Sese Seko
Shugaban ƙasaDR Congo
Karanta ƙarin bayani...Sylvestre Ntibantunganya
Shugaban ƙasaBurundi
Karanta ƙarin bayani...Mohammed Farrah Aidid
Shugaban ƙasaSomaliya
Karanta ƙarin bayani...Mahamane Ousmane
Shugaban ƙasaNijar
Karanta ƙarin bayani...Valentine Strasser
Shugaban ƙasaSaliyo
Karanta ƙarin bayani...Mohamed Said Djohar
Shugaban ƙasaKomoros
Karanta ƙarin bayani...Miguel Trovoada
Shugaban ƙasaSao Tome da Principe
Karanta ƙarin bayani...Dawda Kairaba Jawara
Shugaban ƙasaGambiya
Karanta ƙarin bayani...Ernest Shonekan
Shugaban ƙasaNajeriya
Karanta ƙarin bayani...Joseph Momoh
Shugaban ƙasaSaliyo
Karanta ƙarin bayani...Chadli Bendjedid
Shugaban ƙasaAljeriya
Karanta ƙarin bayani...Justin Lekhanya
Shugaban ƙasaLesotho
Karanta ƙarin bayani...Moussa Traore
Shugaban ƙasaMali
Karanta ƙarin bayani...Mohamed Siad Barre
Shugaban ƙasaSomaliya
Karanta ƙarin bayani...Hissène Habré
Shugaban ƙasaChadi
Karanta ƙarin bayani...Samuel Doe
Shugaban Mulkin SojiLaberiya
Karanta ƙarin labarai...Ahmed Abdallah Abderemane
Shugaban ƙasaKomoros
Karanta ƙarin bayani...Sadiq al-Mahdi
FiraministaSudan
Karanta ƙarin bayani...Habib Bourguiba
Shugaban ƙasaTunisiya
Karanta ƙarin bayani...Thomas Sankara
Shugaban ƙasaBurkina Faso
Labarai masu alaƙa...Jean-Baptiste Bagaza
Shugaban ƙasaBurundi
Karanta ƙarin bayani...Tito Lutwa Okello
Shugaban ƙasaUganda
Karanta ƙarin bayani...Leabua Jonathan
FiraiministaLesotho
Karanta ƙarin bayani...Muhammadu Buhari
Shugaban ƙasaNajeriya
Karanta ƙarin bayani...Milton Obote
Shugaban ƙasaUganda
Karanta ƙarin bayani...Gaafar Muhammad al-Nimeiry
Shugaban ƙasaSudan
Karanta ƙarin bayani...Mohamed Khouna Ould Haidalla
Shugaban ƙasaKaranta ƙarin bayani...Louis Lansana Beavogui
Shugaban riƙon ƙwaryaGuinea
Karanta ƙarin bayani...Shehu Shagari
Shugaban ƙasaNajeriya
...Jean-Baptiste Ouedraogo
Shugaban ƙasaBurkina Faso
Karanta ƙarin bayani...Saye Zerbo
Shugaban ƙasaBurkina Faso
Karanta ƙarin bayani...Goukouni Oueddei
Shugaban ƙasaChadi
Karanta ƙarin bayani...Hilla Limann
Shugaban ƙasaGhana
Karanta ƙarin bayani...David Dacko
Shugaban ƙasaJamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Karanta ƙarin bayani...Sangoulé Lamizana
Shugaban ƙasaBurkina Faso
Karanta ƙarin bayani...Luis Cabral
Shugaban ƙasaGuinea-Bissau
Karanta ƙarin bayani...Godfrey Binaisa
Shugaban ƙasaUganda
Karanta ƙarin bayani...William Tolbert
Shugaban ƙasaLaberiya
Karanta ƙarin labarai...Mohamed Mahmoud Ould Louly
Shugaban ƙasaMurtaniya
Karanta ƙarin bayani...Jean-Bedel Bokassa
Shugaban ƙasa/SarkiJamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Karanta ƙarin bayani...Francisco Macias Nguema
Shugaban ƙasaEquatorial Guinea
Karanta ƙarin bayani...Yusufu Lule
Shugaban ƙasaUganda
Karanta ƙarin bayani...Fred Akuffo
Shugaban ƙasaGhana
Karanta ƙarin bayani...Mustafa Ould Salek
Shugaban ƙasaMurtaniya
Karanta ƙarin bayanai...Idi Amin Dada
Shugaban ƙasaUganda
Karanta ƙarin bayani...Joachim Yhombi-Opango
Shugaban ƙasaKongo
Karanta ƙarin bayani...Moktar Ould Daddah
Shugaban ƙasaMurtaniya
Ƙaranta ƙarin bayani...Ignatius Kutu Acheampong
Shugaban ƙasaGhana
Karanta ƙarin bayani...Ali Soilih
Shugaban ƙasaKomoros
Karanta ƙarin bayani...Tafari Benti
Shugaban ƙasaHabasha
Karanta ƙarin bayani...James Mancham
Shugaban ƙasaSeychelles
Karanta ƙarin bayani...Michel Micombero
Shugaban ƙasaBurundi
Karanta ƙarin bayani...Ahmed Abdallah Abderemane
Shugaban ƙasaKomoros
Karanta ƙarin bayani...Yakubu Gowon
Shugaban ƙasaNajeriya
Karanta ƙarin bayani...François Tombalbaye
Shugaban ƙasaChadi
Karanta ƙarin bayani...Richard Ratsimandrava
Shugaban ƙasaMadagascar
Karanta ƙarin bayani...Gabriel Ramanantsoa
Shugaban ƙasaMadagascar
Karanta ƙarin bayani...Aman Mikael Andom
Shugaban ƙasaHabasha
Karanta ƙarin bayani...Haile Selassie I
SarkiHabasha
Karanta ƙarin bayani...Hamani Diori
Shugaban ƙasaNijar
Karanta ƙarin bayani...Grégoire Kayibanda
Shugaban ƙasaRwanda
Karanta ƙarin bayani...Justin Ahomadegbe- Tometin
Shugaban ƙasaBenin
Karanta ƙarin bayani...Philibert Tsiranana
Shugaban ƙasaMadagascar
Karanta ƙarin bayani...Dakta Kofi Busia
FiraministaGhana
Karanta ƙarin bayani...Milton Obote
Shugaban ƙasaUganda
Karanta ƙarin bayani...Emile Derlin Zinsou
Shugaban ƙasaBenin
Karanta ƙarin bayani...Abdirashid Ali Sharmarke
Shugaban ƙasaSomaliya
Karanta ƙarin bayani...Sarki Idris I
SarkiLibya
Karanta ƙarin bayani...Ismail al-Azhari
Shugaban ƙasaSudan
Karanta ƙarin bayani...Modibo Keita
Shugaban ƙasaMali
Karanta ƙarin labarai...Alphonse Massamba-Débat
Shugaban ƙasaKongo
Karanta ƙarin bayani...Andrew Juxton-Smith
Shugaban ƙasaSaliyo
Karanta ƙarin bayani...Christophe Soglo
Shugaban ƙasaBenin
Karanta ƙarin bayani...David Lansana
JagoraSaliyo
Karanta ƙarin bayani...Siaka Stevens
FiraministaSaliyo
Karanta ƙarin bayani...Nicolas Grunitzky
Shugaban ƙasaTogo
Karanta ƙarin bayani...Ntare na huɗu
SarkiBurundi
Karanta ƙarin bayani...Leopold Biha
FiraministaBurundi
Karanta ƙarin bayani...Kwame Nkrumah
Shugaban ƙasaGhana
Karanta ƙarin bayani...Sarki Mutesa na biyu na Buganda
Sarki/Shugaban ƙasaUganda
Karanta ƙarin bayani...Abubakar Tafawa Balewa
FiraministaNajeriya
Karanta ƙarin bayani...Maurice Yemeogo
Shugaban ƙasaBurkina Faso
Karanta ƙarin bayani...David Dacko
Shugaban ƙasaJamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Karanta ƙarin bayani...Sourou-Migan Apithy
FiraministaBenin
Karanta ƙarin bayani...Moïse Tshombe
FiraiministaDR Congo
Karanta ƙarin bayani...Ahmed Ben Bella
Shugaban ƙasaAljeriya
Karanta ƙarin bayani...Leon M'ba
Shugaban ƙasaGabon
Karanta ƙarin bayani...Hubert Maga
Shugaban ƙasaBenin
Karanta ƙarin bayani...Fulbert Youlou
Shugaban ƙasaKongo
Karanta ƙarin bayani...Sylvanus Olympio
Shugaban ƙasaTogo
Karanta ƙarin bayani...Patrice Lumumba
FiraministaDR Congo
Karanta ƙarin bayani...Abdallah Khalil
FiraministaSudan
Karanta ƙarin bayani...Muhammad VIII al-Amin
SarkiTunisiya
Karanta ƙarin bayani...Muhammad Naguib
Shugaban ƙasaMasar
Karanta ƙarin bayani...Farouk na Masar
SarkiMasar
Karanta ƙarin bayani...
Sabon yayi
Afirka ta fuskanci juyin mulki takwas da suka yi nasara cikin shekara uku da suka gabata. Yayin juyin mulki na baya-bayan nan da aka fuskanta na zuwa ne bayan da sojoji suka farfaɗo bayan shafe kusan shekara 20 rabonsu da yayin juyin mulkin, bayan yayinsa da suka yi a shekarun 1970.
Mutu-ka-raba
Wasu jagororin da suka ƙwace iko, sun yi mulki na gomman shekaru, yayin da wasu kuma aka tumɓuke su cikin kwanaki bayan kwace mulkin.

Alal misali Shugaban ƙasar Equatorial Guinea, Obiang Nguema ya shafe shekara 44 yana mulki bayan ƙwace iko a shekarar 1979.

A yanzu shi ne shugaban ƙasa a Afirka da yafi jimawa a kan mulki.
Shugabannin da suka sake komawa bayan kifar da su

Juyin mulki a Yammacin Afirka da yankin Sahel
Mafi yawan ƙasashen yankin Sahel sun fuskanci juyin mulkin soji. Juyin mulki na baya-bayan nan a yankin shi ne wanda aka yi a Jamhuriyar Nijar da Gabon a 2023
Shugabannin soji sun kuma ƙwace mulki a Mali a 2020 da 2021 da Chadi da Guinea da Sudan a 2021. Burkina Faso ta fuskanci juyin mulki har sau biyu a 2022, Duka waɗannan ƙasashe rainon Faransa ne, in ban da Sudan.
Tun 2000, kashi uku cikin huɗu na juyin mulkin da suka samu nasara a Afirka sun auku ne a ƙasashe rainon Faransa. Hakan ya sa wasu ke aza ayar tambaya cewa ko tasirin Faransa a Afirka ne ke haddasa hakan.
Juyin mulkin da suka yi nasara a Afirka tun 1952
Mafi yawan ƙasashen Yammacin Afirka da na Tsakiya sun fuskanci yawan juyin mulkin da ya yi nasara. Kusan rabin ƙasashen yankin 17 sun fuskanci aƙalla juyin mulki huɗu a Yammacin Afirka
Burkina Faso ce ta fi kowace ƙasa yawan juyin mulki a Afirka inda ta fuskanci takwas, daga nan sai Saliyo da Uganda masu bakwai kowannensu.
Kashi ɗaya cikin uku na ƙasashen Afirka, mafi yawancinsu daga Gabashi da Kudanci Afirka ne ba su taɓa fuskantar juyin mulkin da ya yi nasara ba
Mai shekara 34, a 2024, Ibrahim Traore ya kasance shugaban ƙasa mafi ƙanƙantar shekaru a duniya. Ya zama shugaban riƙon ƙwarya na Burkina Faso bayan da sojoji suka yi juyin mulki ranar 30 ga watan Satumban 2022, inda suka kifar da gwamnatin riƙon ƙwarya ta Paul-Henry Sandaogo Damiba.
Kwace mulki
Kusan kashi 90 na juyin mulkin da suka yi nasara a Afirka, sojoji ne suka yi, daga nan sai sojojin haya masu kashi huɗu. Sauran nau'ikan juyin mulki da ka yi a Afirka sun ha ɗa da boren fararen hula, mulkin mallaka, dakarun tawaye da juyin mulkin masarauta.
Gaba kura baya tsayaki
Mafi yawan shugabannin da suka karɓi mulki da ƙarfi, daga baya wasu ne ke hamɓarar da su, a wasu lokuta ma a kashe su

A 1972 Janar Ignatius Kutu Acheampong ya jagoranci juyin mulki da babu zubar da jini, wajen tumbuƙe zaɓaɓɓiyar gwamnatin Firaministan Ghana Dakta Kofi Busia. Shekara shida bayan haka aka tuɓuke shi a wani juyin mulkin masarauta sannan kuma aka kashe shi shekara guda bayan haka.

Thomas Sankara ya zama shugaban Burkina Faso a 1983, bayan wani juyin mulki da sojoji suka yi a madadinsa, a lokacin da yake ƙarƙashin ɗaurin talala. A ranar 15 ga watan Oktoban 1987 wata ƙungiyar masu ɗauke da makamai suka kashe Sankara a lokacin wani juyin mulki da Blaise Compaore ya jagoranta.

Gaafar Nimeiry ya tunɓuke shugaban Sudan Ismail al-Azhari a 1969, sannan ya karɓe iko, da farko a matsayin shugaban mulkin soji, sannan ya zama shugaban ƙasa, kafin a kifar da gwamnatinsa a 1985.

Jean-Baptiste Bagaza ya tumɓuke shugaban ƙasar Burundi Michel Micombero a 1976 sannan ya karɓe mulki. shekara 11 bayan hakan ne kuma aka hamɓarar da shi, lamarin da tilasta masa gudun hijira.

Omar al-Bashir ya zama shugaban ƙasar Sudan a 1989 a lokacin da yake muƙamin Burgediya Janar a rundunar sojin ƙasar, ya jagoranci sojoji wajen kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatim ƙasar. Daga nan ya ci gaba da zama shugaban Sudan har zuwa 2019 lokacin da wani juyin mulkin soji ya kifar da gwamnatinsa.

François Bozizé Yangouvonda ya ƙwace mulki a 2003. Inda ya zama shugaban ƙasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka. Shekara 10 bayan haka aka hamɓarar da shi.

Barinsa a cikin dangi

Ƙwace mulki al'ada ce ta dangi a wasu ƙasashen. Alal Misali a Equatorila Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo - wanda ɗan ɗan'uwan shugaban ƙasar Francisco Macias Nguema - ne ya yi masa juyin muyin mulki a 1979. Zuwa shekarar 2024 Teodoro ne shugaban ƙasa - wanda ba na sarauta ba - na biyu mafi jimawa a karagar mulki.

Laurent Kabila ya hamɓarar da Shugaba Mobutu Sese Seko a 1997, sannan ya zama shugaban DR Kongo na uku. Daga baya kuma ɗansa mai shekara 29, Joseph Kabila ya gaje shi bayan da ɗaya daga cikin masu kare lafiyarsa ya kashe shi.





































































































































Juyin mulkin Gabon: Sojoji sun ƙwace mulki daga Ali Bongo, sannan suka yi masa daurin talala
Juyin mulkin Nijar: Shin Faransa ce ke janyo rashin zaman lafiyar Yammacin Afirka
Juyin Mulkin Burkina Faso: Shugaban da aka hamɓarar Damiba a Togo