Masu shirya fina-finan 'yan Najeriya da ka iya shan ɗauri saboda fim ɗin maɗigo mai suna Ife

Photo cover of Ife showing two women facing each other

Asalin hoton, PAmela Adie

    • Marubuci, Daga Azeezat Olaoluwa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Women's Affairs Reporter, West Africa

Wasu masu shirya fina-finai biyu na fuskantar yiwuwar ɗauri idan suka yi burus da tsattsauran gargaɗin da hukumomi suka yi masu, suka ci gaba da shirye-shiryen fitar da wani fim da ke nuna wasu mata biyu suna soyayya.

Ita kanta tababar da aka yi tsakanin masu shirya fina-finan da hukumar da ke sa ido kan fina-finan a Najeriya NFCVB ta ci a yi fim a kanta.

Mai shirya fina-finai Pamela Adie da mai ba da umarni Uyaiedu Ikpe- Etim sun ɗaura ɗamarar fitar da fim din mai suna 'Ife' (wanda ke nufin "soyayya" a Yarabanci) ga 'yan Najeriya, amma NFVCB ta ce ba za ta amince ba saboda fim ɗin ya saba wa dokokin ƙasar kan madigo da luwaɗi.

Nuna fim

Don samun damar nuna fim ɗin, masu shiryawar na shirin fitar da shi a shafukan intanet don yi wa masu sa idon ba-zata. Sai dai NFVCB na matuƙar sa ido kan duka hanyoyin shafukan intanet don hana fim ɗin fita.

A cewar shugaban NFVCB Adebayo Thomas, Adie da Ikpe-Etim na iya shan ɗauri bisa laifin nuna luwaɗi da maɗigo a ƙasar da aka haramta su kuma wanda aka kama da laifin haka na iya zaman gidan kaso tsawon shekaru 14.

Suna shirya nuna fim ɗin cikin sirri a birnin Legas a karshen wannan watan, wanda kuma suke ganin za su iya yi ba tare da samun izini ba.

Haka kuma, za a haska fim ɗin Ife a Canada a watan Oktoba.

Mai shirya fim din Ife

Adie ta ce manufar fim ɗin shi ne a nuna gaskiyar yadda rayuwar 'yan maɗigo take a fina-finan Najeriya.

Idan aka nuna mace 'yar maɗigo a fim ɗin Nollywood, ana nuna su a matsayin masu shafar aljannu ko kuma ƙawayen da ba na kirki ba sun ja ra'ayinsu ko kuma an turasasa masu fara maɗigon, sannan ana nuna cewa suna ɓukatar a kuɓutar da su daga wannan hanya, a cewarta.

"Da wuya ka ga labari kan mata ko maza 'yan luwaɗi, musamman ma mata.

"An haɗa fim ɗin Ife ne don gyara wannan giɓin sannan a sa mutane su fara tattauanawa kan wannan batu a Najeriya."

Me fim din Ife ya kunsa?

Ife labari ne kan wasu mata biyu da suka kamu da son juna yayin da suka yi zaman kwana uku tare. Sai "suka fuskanci matsaloli da ke tattare da soyayya tsakanin mace da mace a kasa kamar Najeriya", a cewar wata sanarwa kan fim din.

Babu shakka fim din ya nuna abubuwan da dama da suka kunshi luwadi da madigo.

Two actors on the set of Ife are sat on a couch

Asalin hoton, Pamela Adie

Bayanan hoto, Uzoamaka Aniunoh da Cindy Amadi a wajen daukar fim din inda suka fito a mata biyu masu soyayya d juna

A wani bangare na fim din, matan biyu, Ife da Adaora na kwance a gado suna magana kan soyayya da kalubalen da 'yan luwadi da madigo ke fuskanta musamman daga iyalansu.

Tattaunawar tasu ta zama ginshikin tallar fim din.

"Na fara gaya wa mahaifiyata, sai da ta yi kusan mako guda kafin ta amince," in ji Ife, wadda Uzomaka Aniunoh ta taka rawa, inda take ,magana kan yadda ta bayyana wa mahaifiyarta cewa ita 'yar madigo ce.

"Ba baun mamaki ba ne wannan dngane da iyaye mata a Najeriya." in ji Adaora, wadd Cindy Amadi ta taka rawa.

"Na yi gaggawar cewa ina kaunarki?" Adaora ta tambayi Ife a lokacin da suke rungume da juna.

"Mu 'yan madigo ne, yanzu ne lokacinmu," a cewar Ife.

'Dole ne a tantance shi'

Madigo da Luwadi manyan abubuwa ne da ke janyo ce-ce-ku-ce sosai a bangarori da dama a Afrika.

Afrika nahiya ce da addini da al'ada suke da tasiri, kuma addinin Kirista da na Musulunci sun haramta madigo da luwadi.

A dalilin haka, Najeriya na daya daga cikin kasashe 30 a nahiyar da ake kama masu aikata su.

An kafa dokar da ke haramta soyayya ko auren jinsi daya a shekarar 2014 a Najeriya. 'Yan sanda a kasar sun sha kama wadanda ake zargi da aikata madigo da luwadi, inda mafi yawansu suke buya.

Mai shirya fim din Ife

Nuna wariya da bukatar a kalubalanci masu nuna madigo a matsayin abin assha na cikin abubuwan da suka zaburar da mai ba da umarni Ikpe-Etim ta yi wannan fim din.

"Kafin yanzu, an sha gaya mana labarai da ba na gaskiya ba. Abin da muke so mu cimma a wannan fim din shi ne mu sauya tunanin mutane kan 'yan luwadi da madigo. Muna so soyayyar jinsi daya ta zama gama gari.

"Fim din nan zai goge kunyar da ke tattare da soyayyar jinsi daya da mata ke fuskanta," kamar yadda ta shaida wa BBC.

Soyayya ko auren jinsi daya a Afrika na kara samun tagomashi, saboda shafukan intanet da ke ba da damar tattaunawa da fina-finai.

Presentational grey line

Amma wannan bai hana masu shirya fina-finai karawa da hukumomi ba.

Shugaban NFVCB ya ce babu wata dama ga fim din Ife ko wani fim mai magana kan soyayyar jinsi daya a Najeriya.

"Akwai dokar da ta hana madigo da luwadi, ko a gaske ko a fim ko a wasan dandali. Idan fm ne da aka shirya a Najeriya, dole a tace shi," a cewar Mista Thomas.

Ya ce a ko wane bangare ne, "muddin a Najeriya aka shirya shi kuma labarin Najeriya ake bayarwa to dole ne mu tace shi".

A man stands in a shop selling Nollywood films

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ife ba fim din da aka saba gani ba ne a masana'antar fina-finan Najeriya

Amma babu wani shirin haska fim din Ife a silmomin Najeriya da mutane da yawa, ko kuma sayar da shi a faifan bidiyo, saboda masu shirya fim din na so ne su sake shi a intanet.

Amma ko wannan din ma na iya janyo masu matsala da masu sa ido.

Auren jinsi daya na kara samun karbuwa

"Idan fim din bai bi ta hannun NFVCB ba kuma aka fitar da shi, masu shirya fina-finan na iya fuskantar dauri," a cewar Mista Thomas.

"Matsawar a Najeriya aka shirya shi, za mu cire shi saboda muna hada kai da Google da Youtube da sauran masu ruwa da tsaki."

Amma wannan bai sagar da gwiwowin masu masu shirya fim din ba kuma Adie ta ce tawagarta za ta ci gaba da shirye-shiryenta saboda sun yi amannar cewa ba su aikata wani laifi ba kuma ba za su nemi izinin fitar da fim din a shafukan intanet ba.

Ba wannan ne karon farko da wani fim kan auren jinsi daya ya jawo karawa da hukumomi a nahiyar ba.

An haramta fim din Stories of Our Lives, kan soyayyar jinsi daya a Kenya a 2014 saboda "saba wa dokokin kasa".

Haka ma fim din Rafiki na Kenya wanda ya nuna mata biyu suna soyayya, wanda ya zama fim na farko a yankin Afrika ta Gabas da aka haska a bikin haska fina-finai na Cannes sannan aka zabe shi a matakin farko a bikin fina-finai na Oscar.

An haramta fim din Inxeba/The Wound na Afrika ta Kudu da ya nuna soyayya tsakanin maza biyu a kasar a shekarar 2018.

Duk da wannan koma bayan, wasu kungiyoyin masu auren jinsi daya a Afrika sun ce suna samun karbuwa a hankali kuma sun danganta haka da bayyana labaransu da ake yi a fina-finai da littafai da ke nuna amfaninsu ga yara masu tasowa.

Wani bincike da aka yi a shekarar 2019 ya nuna cewa an samu karuwar mutane masu amincewa da 'yan madigo da luwadi - duk da cewa wadanda ba su amince da su ba sun fi yawa.

Kashi 60 cikin dari na 'yan Najeriyar da aka yi binciken a kansu sun ce ba za su amince da wani dan uwansu ba idan dan luwadi ne ko madigo, amma wadannan alkaluman sun ragu idan aka hada da kashi 83 cikin dari a shekarar 2017.

Bukatar kawo sauyi na daga cikin abubuwan da suka sa mutane irin su Ikpe-Etim ke son ci gaba da ba da labarin masu son auren jinsi daya.

"A mtsayina na dan kungiyar da ake warewa, kullun kana cikin zullumin mutane za su yi maka mummunar fahimta.

"Na san cewa idan ina so al'uma ta ga masu sha'awar aren jinsi daya a wata hanya ta daban, dole ne in bayar da cikakken labarinsu," a cewarta.