Ghana: An bai wa 'yan kasuwar waje wa'adi

Asalin hoton, AFP
Gwamnatin Ghana ta bai wa kananan 'yan kasuwa daga kasashen waje wa'adi zuwa ranar 5 ga watan October da su fice daga kasuwannin kasar.
Ghana ta hana wadannan 'yan kasuwa ne gudanar da harkokin kasuwanci a wasu kasuwannin wasu biranen kasar da suka hada da Accra da Kumasi.
Gwmnatin ta ce 'yan kasar Ghana ne kadai ke da ikon gudanar da harkokin kasuwanci a wadannan kasuwanni.
Tuni dai wasu 'yan kasuwar da suka fito daga Nigeria suka fara korafi dangane da wannan mataki da gwamnatin kasar ta dauka.







