Zargin tafka magudi a zaben Afghanistan

Asalin hoton, AFP
Dan takarar shugaban kasa a Afghanistan Abdullah Abdullah ya yi watsi da sakamakon zaben da aka sanar yana zargin cewa a tafka magudi.
Mr Abdullah ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa wadanda suka taru a tsakiyar birnin Kabul, inda ya yi ikirarin cewa shi ya kamata a ba nasara a zaben da a aka gudanar.
Dan takarar shugaban kasar ya kuma yi Allahwadai da zaben inda ya jaddada cewa shi da magoya bayansa ba za su taba amincewa da wannan sakamakon ba.
A bangare guda kuma Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce duk wani mataki da aka dauka na karbe mulki ba bisa ka'ida ba a kasar ka iya janyowa Amurka ta dakatar da tallafin da take baiwa Afghanistan.







