Peter Obi: 'Ba na son a zabe ni don na fito yankin Kudu maso Gabas'

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Dan takarar shugaban Najeriya a Jam'iyyar Labour Peter Obi, ya ce ba ya so mutane su zabe shi domin ya fito daga yankin Kudu maso Gabashin kasar.

A wata hira ta musamman da ya yi da BBC, Mista Obi ya ce ya tsaya takara ne domin shi dan Najeriya ne mai 'yancin yin hakan.

Haka kuma ya yi tsokaci kan batun magoya bayansa da ke cin mutuncin mutane a shafukan sada zumunta, inda ya ce yawancin su ba masoyansa na tsakani da Allah ba ne.

Yin hirar da daukar bidiyo da tacewa: Abdulbaki Aliyu Jari