Yadda Mahajjata ke jifan Shaidan a ranar karshe ta aikin Hajj

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Mahajjata da ke aikin Hajji na shekarar 2022 na jifar Shaidan a rana ta uku.

Wannan dai shi ne kusan ibada ta karshe da mahajjatan su ke yi daga cikin manyan ibada da ake gudanarwa.

Baya ga jifan, wasu daga cikin alhazan na komawa Makka domin dawafin bankwana inda akasarinsu kuwa ke tafiya Madina domin ziyara.

"Yan Najeriya na daga cikin dubban mahajjata da suke gudanar da aikin Hajji na shekarar 2022.

A wannan shekarar, an kayyade yawan mahajjata da ko wace kasa ta tura aikin Hajji a kasar Saudiyya sakamakon cutar Korona.