Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba na tsoron 'yan takarar PDP da APC a zaben shugaban kasa - Kwankwaso
Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A ranar Talata 31 ga watan Mayu ne jam'iyyar NNPP a Najeriya ta tantance ɗan takarar shugaban ƙasarta Rabi'u Musa Kwankwaso.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa jim kaɗan bayan kammala tantancewar, Sanata Kwankwaso ya ce bai kai ga tsayar da wanda zai zama mataimakinsa ba tukunna.
Ya ce sai bayan an yi babban taron jam'iyyar na ƙasa sannan masu ruwa da tsaki na NNPP za su haɗu a yi shawarar wanda zai yi masa mataimaki a takarar.
Sannan a cikin hirar Kwankwaso ya ce ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun APC da PDP ba sa ba shi tsoro a aniyarsa.