Yadda Indiyawa ke faɗi tashin neman halal ɗinsu a cikin tsananin zafi

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Rayuwa a wajen aikin gine-gine na da matuƙar wahala, amma ga Tundre mai shekara 29, ya zama dole a gare shi ya ci gaba da aikin a cikin tsananin yanayin zafi.

Indiya na fuskantar tsananin zafi da yake kai wa maki 49.2C ma’aunin selshiyas.

Tundre wanda ke zaune a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin ƙasar, ya bayyana yadda rayuwa take a cikin tsananin zafin.