Ranar Maleriya ta Duniya: Hanyoyin kamuwa da maleriya da yadda za a kauce wa cutar

Bayanan bidiyo, Ranar Maleriya ta Duniya: Hanyoyin kamuwa da maleriya da yadda za a kauce wa cutar

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Wata kwararriya likita a Najeriya ta bayyana matakan da ake bi wajen kamuwa da cutar maleriya.

A hirarta da BBC Hausa, Dokta Amira Aliyu Aminu, ta kuma zayyana hanyoyin da za a bi domin kauce wa kamuwa da cutar.

Ta yi bayanin ne a yayin da a yau, 25 ga watan Afrilu, ake tunawa da Ranar Maleriya ta Duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ware ranar ce domin wayar da kan jama'a game da yadda za a kawo karshen wannan cuta a fadin duniya.