Abin da ya sa na gabatar da kudurin dokar cin tarar 'yan Daudu - Umar Muda Lawal
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ƴan Daudu musamman maza masu shiga irin ta mata da mata da ke shiga irin ta maza za su fuskanci hukunci a Najeriya.
Wannan na cikin wani ƙuduri da aka gabatar a gaban Majalisar Wakilan Najeriya da ke son a yi wa Dokar Haramta Auren Jinsi kwaskwarima inda wani ɗan majalisa ya nemi a haramta daudu a ƙasar.
A ranar Talata ne 'yan majalisar suka yi wa ƙudirin karatun farko. Sai sun yi karatu na biyu da na uku sannan ya zama doka.
Ɗan majalisa mai wakiltar Toro daga Jihar Bauchi, Umar Muda Lawal ne ya gabatar da kuɗirin a majalisar inda ya nemi a haramta daudu a fili ko kuma a ɓoye.
Ku saurari hirar Honorabul Umar Muda Lawan a wannan bidiyon don jin cikakken dalilin d aya sa ya gabatar da ƙudurin dokar.
Karin labari mai alaƙa