Ƴan sama jannatin Rasha da Amurka sun ce lafiya lau suke zaune a sararin samaniya

Bayanan bidiyo, Ƴan sama jannatin Rasha da Amurka sun ce lafiya lau suke zaune a sararin samaniya

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani Ba'amurke tare da wasu Rashawa biyu - wadanda dukkansu 'yan sama jannati ne - sun dawo duniyarmu ta Earth daga tashar ƙasa-da-ƙasa da ke can cikin sararin samaniya.

Hakan ya faru ne yayin da dangantaka tsakanin Rasha da Amurka ke ƙara tsami kan yaƙin ƙasar Ukraine.

Wata rokar Soyuz mallakin ƙasar Rasha ce ta dawo da Mark Vande Hei na hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA, tare da Anton Shkalerov and Pyotr Dubrov 'yan kasar Rasha, inda ta sauka a wani yankin da ke tsakiyar kasar Kazakhstan.

An dai rika fargabar cewa Rasha za ta ƙi ɗauko Ba'amurken daga tashar sararin samaniyar -- sai dai da wuya Amurka ta sake neman taimakon Rasha wajen jigilar 'yan sama jannatinta.

Ba'amurken ya kafa tarihi a matsayin mutumin da ya fi daɗewar zama a wajen duniyarmu, inda ya shafe kwana 355 yana rayuwa a sararin samaniya.

Ga ƙarin bayani kan tashar ƙasa da ƙasa da ke zagaya duniya daga sararin samaniya