Abin da ya sa matan Sudan suka sake fita zanga-zanga duk da 'kashe su da ake yi'

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An shafe makonni ana zanga-zangar ƙin jinin mulkin soja a Sudan, bayan hamɓare gwamnatin farar hula a watan Oktoban 2021.

Kusan mutum 80 aka kashe a wuraren zanga-zanga, a cewar ƙungiyoyin agaji, sannan wasu da dama sun mutu sakamakon harbin su da aka yi.

Dakarun tsaron Sudan sun sha musanta cewa suna amfani da harsashi a kan masu zanga-zangar lumana.

Matan Sudan, wadanda suka taka muhimmiyar rawa a boren 2019 da aka hamɓarar da Omar Al-Bashir sun sake bazama kan tituna don yin zanga-zanga.

Wasu daga cikinsu hakan ya zama ajalinsu.