Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyo: Gobara ta cinye dimbin dukiya a Unguwar-guragu a Abuja
Wata gobara ta tashi dazu da rana a unguwar guragu da ke Karmajiji a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Gobarar ta kone matsugunai da dama na mazauna yankin mafi yawansu masu nakasa a kafa.
Wasu da lamarin ya shafa sun ce sun yi mummunar asara, inda yawancinsu suka ce ba su tsira da komai ba sai kayan jikinsu.
Wata mata, Fatima, ta ce kudinta da suka kai tsabar naira dubu 500 sun kone a gobarar, da sarkarta ta gwal, da tufafinta kusan guda 100 da sauran kayanta na aure.
Babu dai asarar rai ko jikkata a cikin gobarar.
Mazauna unguwar wadanda sun hada da masu larurar kafa da kuma ta ido da iyalansu, suna zaman wucin-gadi ne a unguwar ta Karmajiji tsawon shekaru da dama.
Sarkin masu bukata ta musamman na Abuja Alhaji Muhammad Sulaiman ya yi kira ga hukumomin Abuja da su gaggauta gina musu gidajensu na dundundun a filin da aka ware musu a Gwagwalada.
Mazauna unguwar sun ce wannan ne karo na uku da aka samu gobara a unguwar ta Guragu a Karmajiji a cikin shekara bakwai.
Kuma a gobarar da aka fuskanta a shekarun baya an samu asarar rayuka biyu, kamar yadda mazauna unguwar suka bayyana.
Bidyo: Bashir Idris
Tacewa: Yusuf Yakasai