Yahudawan da ke shigar burtu a matsayin Musulmai don shiga Masallacin Kudus

Wasu Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi sun ce suna yin shigar Musulmai don samun damar yin ibada a masallacin Ƙudus mai tsarki da ake matuƙar taƙaddama akansa.

Bayan Isra'ila ta kama gabashin birnin Ƙudus a 1967, an amince cewa a ci gaba da tafiya kamar yadda ake a baya: wato waɗanda ba Musulmi ba za su iya ziyartar masallacin, amma ba za su yi ibada ba.

BBC ta tattuna da wani Bayahuden Isara'ila mai ra'ayin riƙau Raphael Morris, wanda ya jagoranci wata ƙungiya mai suna "Returning to the mount", wacce take fafutukar yin ibada a wajen mai tsarki, haka kuma ta yi magana da wata mai fafutuka Musulma Bafalasɗiniya Hanady Halawani wacce ta ce za ta kare masallacin na Ƙudus.

Shirya Bidiyo: Gidi Kleiman, da Yolande Knell da Youssef Shomali

Ɗaukar bidiyo da tacewa: Anastassia Zlatopolskai

Fassarawa da haɗawa: Fatima Othman