Zamantakewa: Matakan da iyaye za su dauka don dakile yawan sace ‘ya’ya da ake yi

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A wannan kashi na 24, shirin ya yi duba ne kan irin matakan da iyaye za su dauka don dakile yawan sace ‘ya’ya da ake yi.

A matsayinki na Uwa ko a matsayinka na Uba akwai wani tashin hankali ko rudani da ya zarce wata rana ki waye gari, ko ka wayi gari da labarin banta yayanku?

Ina ga a duniya idan akwai abin da kan ɗagawa iyaye hankali to bai wuce labarin ɓatan ƴaƴansu ba.

Batan ƴaƴa babbar musiba ce da ke sa iyaye a cikin ruɗu, don har su kan gwammmace mutuwa ƴaƴan suka yi suka suturta gawarsu da ace ba a san inda suke ba.

Me za mu yi a matsayinmu na iyaye don gujewa samun kanmu a cikin irin wannan matsala? Batun da za mu tattauna kenan a filin zamantakewa na wannan makon

A mafi yawan lokuta a gidaje a yankunanmu za a ji iyaye na cewa yara, ku fita gidan makwabta kun ishe ni, ku fita ku yi wasanku a waje kar ku dame mu.

Su kan fadi hakan ne don tsabar yakinin da suke da shi cewa inda suke tura yaran ba waje ne mai barazana ba, amma fa a ganinsu.

An zo zamanin da kusan komai da ke kewaye da kai kan iya zama barazana, don haka sai mun dinga zama masu kaffa-kaffa a kan komai.

A cikin shirin, mun yi hira da wata uwa da ta gaya mana irin mummunan yanayin da ta shiga lokacin da aka sace mata ɗa.

Ba so muke mu ɗora wa iyaye laifi ba, sai dai fa ku sani cewa, akwai abubuwan da muke ganinsu ƙanana, amma dole akwai buƙatar sa idonmu da yin taka tsantsan, kamar dai yadda Ustaz Aliyu Rashid Makarfi ya yi kira a kai.

Ita ma uwar nan ta bai wa iyaye shawarar ɗaukar karin matakan kula.

Muna fatan waɗannan shawarwari za su yi tasiri a zuƙatan iyaye.