‘Na gwammace mutuwa a teku da na ci gaba da zama a Afirka’

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Fiye da ƴan cirani 17,000 da masu neman mafaka ne suka tsallaka tekun Ingila zuwa yanzu a hekarar nan ta 2021, duk da ƙoƙarin da hukumomi ke yi tun a bara don hana irin wannan kasadar.

Wasu daga cikinsu kan adana dubban fama-famai don biyan masu fasa ƙwauri su shirya musu yadda za su tsallaka ba bisa ƙa’ida ba.

Amma da yawansu, musamman matasan cikinsu da ke tafiya su kaɗai, ba su da kuɗi kuma ba su san kowa ba a Calais, sannan ba su da wasu isassun bayanai idan har suka samu isa can ɗin.

Cikin shekara ɗaya da ta gabata, BBC ta ɗauki bidiyon wasu tarin matasa ƴan ci rani daga Sudan waɗanda suka wuce gona da iri wajen ƙoƙarin isa Birtaniya.

Ɗaukar bidiyo: Julien Goudichaud da Daisy Walsh