Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sanata Uba Sani ya bayyana dabarun da za a farfado da darajar Naira
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ɗaya daga cikin manyan matsalolin da mahukunta ke fadi-tashin magancewa a Najeriya ita ce matsalar faɗuwar darajar Naira.
Babban Bankin ƙasar ya dauki matakai da dama, amma har yanzu matsalar ba ta kau ba.
Sai dai shugaban kwamitin kula da harkokin bankuna na majalisar Sanata Uba Sani, a tattaunawarsu da Ibrahim Isa ya ce faɗuwar darajar nairar na da alaƙa da tabarbarewar tsaro, kuma sai Najeriyar ta inganta tsaro masana'antu za su rayu har su samar da kayan da za a yi safararsu zuwa ƙasashen waje.
Sanata Uba Sani, dan majalisar dattawa ne daga jihar Kaduna, kuma shugaban kwamitin majalisar a kan harkokin bankuna.