Yadda al’umma ke rayuwa ba sadarwa a Zamfara

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Al'ummar a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na ci gaba da rayuwa ba sadarwa.

Kwana 12 kenan da katse hanyoyin sadarwa a jihar, ɗaya daga cikin matakan da hukumomi suka ɗauka na tsaro domin magance matsalar ƴan bindiga da suka addabi Zamfara da makwabtan jihohi.

Yawancin al’ummar Zamfara na nuna goyon bayansu ga matakan tsaron da mahukuntan jihar suka dauka musamman toshe kafafen sadarwa a jihar wanda matakin ya shiga mako na biyu.

Hakan kuwa matakin ya kawo wajen gudanar da rayuwar yau da kullum a jihar.

Amma kuma duk da haka mutane a babban birnin jihar sun ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda aka saba, yayin da jami'an tsaro ke can a dazuka suna fatattakar "yan fashin dajin.

A bayyane take dai cewa al'ummar jihar na cike da fatan cewa wannan shi ne fadan tashi tsakanin dakarun Najeriya da kungiyoyin 'yan bindaga da suka mayar da wannan matashiyar jihar mai albarkar kasar noma da dimbin ma'adinin zinare wata mayankar bil adama.