Sauyin yanayi: Kona gas yana ruruta yanayin zafi a kudancin Najeriya

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Joy da iyalanta na daga cikin 'yan Najeriya miliyan biyu da ke rayuwa kilomita hudu kusa da inda ake kona iskar gas a yankin kudancin kasar mai arzikin man fetur.

Joy ta ce a lokacin da take karama yanayin kasar ba mai tsananin zafi ba ne kamar yanzu.

Sauyin yanayi na da matukar tasiri a kan Najeriya.

Kasar noma a yanzu tana zama tamkar ta Sahara, yayin da ambaliyar ruwa ke karuwa a kudancin kasar.

Bangaren masana'antar man fetur na lalata abubuwa musamman ma kona iskar gas - gas din da ke konewa wanda yake fita ne a lokacin da ake hako mai daga kasa - kuma hakan ya saba doka a Najeriya.