Bidiyo: Dattijo mai shekara 90 ya koma gida Jigawa bayan ya yi ci-ranin shekara 40
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta sake hada wani dattijo mai shekara 90 da iyalinsa a jihar Jigawa da ke Najeriya bayan tsawon shekaru.
Dattijon mai suna Alhaji Abdullahi, wanda mutumin kauyen Mai Mazari ne, ya tafi ci-rani fiye da shekaru 40 da suka gabata.
Ya ce ya tafi ci-rani a kasar Sudan inda ya rika noma da kiwo, yana mai cewa bayan ya tara kudi ya tafi Saudiyya a kasa domin sauke farali.