Halima Zawiya: Matashiyar da ta rungumi harkar noma a Jigawa
Latsa wannan hoton da ke sama domin kallon hira da Halima:
Hausawa kan ce kallabi tsakanin rawuna domin misalta macen da take yin wani aiki da ake kallon na ‘ya’ya maza ne.
Kuma wannan karin magana ya dace da matashiya Halima Zawiya, mai shekara 24 'yar jihar Kano, wadda take aikin na-duke wato noma.
Halima, wadda take da digiri kan fannin noma, ta zabi komawa gona domin dabbaka abin da ta karanta a jami’a.
Matashiyar na da makekiyar gonar shinkafa a jihar Jigawa inda take noman rani da na damina domin noman kayan miya da shinkafa.
A wannan karo BBC ta je gonar ta Halima mai girman kadada 70 domin ganin yadda za ta girbi amfanin da ta shuka.