Babagana Zulum: Gwamnan Borno ya ce ba ya tsoron mutuwa
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce ba ya tsoron mutuwa shi ya sa yake shiga duk wurin da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu suke zaune.
Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da BBC Hausa.
Da aka tambaye shi kan dalilin da ya sa yake zuwa yankuna masu hatsari wadanda aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram, har ma yakan kwana, sai Gwamna Zulumm ya ce "mutane su gane cewa raina sai lokacin da Allah ya ce zai fita sannan zai fita.
"Babu wani dan adam da ba ya son ransa, amma ka duba dubban mutanen da suke shan wahala; ka tabbatar cewa duk gun da Boko Haram suka ci mutane, ni koma meye zan shiga", in ji gwamnan jihar ta Borno.
Ya kara da cewa sun je Damasak sun zauna inda dubban mutane suka koma gidajensu daga wuraren kamar Jamhuriyar Nijar, yana mai cewa "shi ya sa ba za mu ji tsoro ba, Allah zai kiyaye kuma idan kwana ya kare Allah Ya sa mu cika da imani."
A baya dai, wasu mayaka masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyar IS sun kashe jami'an tsaro goma sha biyar a wani kwanton bauna da suka yi wa tawagar Gwamna Zulum.
Daga cikin wadanda suka rasa ransu a wannan hari akwai 'yan sanda takwas da sojoji uku da kuma 'yan kungiyar 'yan sintiri da ke tallafawa dakarun gwamnati wato Civilian JTF hudu.
Gwamnan jihar ta Borno, Babagana Umara Zulum, da tawagarsa na kan hanyarsu ne ta zuwa garin Baga a lokacin da aka kai musu harin.
Bayan haka, akwai lokacin da masu tayar da kayar bayan suka yi amfani da jaki wajen kai wa gwamnan jihar ta Borno Babagana Umara Zulum hari.
A lokacin, Kwamishinan Shari'a na jihar Borno, Barista Kaka Shehu Lawan, wanda yake cikin tawagar gwamnan da ta tsallake rijiya da baya a hare-hare biyu, ya shaida wa BBC cewa harin farko ya faru ne bayan sun tashi daga Monguno zuwa Baga.