Yadda Isra'ila ta ruguza wani bene a birnin Gaza

Wannan ne lokacin da harin Isra'ila ya ruguza wani bene a birnin Gaza.

An gargadi mutane da su fice daga cikin benen gabanin kai harin.

Kungiyar Hamas ta mayar da martani da harba rokoki kan birnin Tel Aviv da ke Isra'ila.

Rikicin ya yi kamari ne bayan kwashe kwanaki ana arangama a yankin.