Amfani da hotunan tauraron ɗan adam don aika wa mabuƙata tallafin kuɗi

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Amfani da hotunan tauraron ɗan adam don aika wa mabuƙata tallafin kuɗi

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A yayin da cutar korona ta ɓulla a Togo a watan Maris ɗin bara, kamar dai ko ina a duniya, shugabanninta sun umarci ƴan ƙasar su zauna a gida tare da aika tallafin kuɗi na gaggawa ga waɗanda ke cikin buƙata sosai.

Sun yi hakan ne ta hanyar amfani da wani sabon tsari da ya haɗa da neman inda mabuƙatan suke a hotunan na’urar tauraron ɗan adam.

Sai kuma aka dinga tura wa mutane kuɗin ta wayoyin salularsu.