Nawal El Saadawi: Waiwaye kan rayuwar fitacciyar mai kare hakkin mata ta Masar

Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don kallon bidiyon:

Dr Nawal El Saadawi fitacciyar mai rajin kare haƙƙin mata ce da ta yi suna a duniyar Larabawa.

Bayan mutuwarta a lokacin da take da shekara 89, mutane da dama a faɗin duniya sun yi ta tuna wa da rubuce-rubucenta da aikinta na malanta da aikinta na likitanci.

Ta jawo ce-ce ku-ce a yankinta kan yadda take kallon batutuwan haƙƙoƙin mata inda ta sha suka da kuma tsallake wa barazanar kisa.

Ƙarin labarai masu alaƙa