'Yadda riƙon marainiya ya zame min alheri'

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Bayan kwashe tsawon shekaru da yin aure ba ta samu haihuwa ba, Hafsat Muhammad Sani da mijinta sun ɗauko maraininya daga gidan marayu da niyyar riƙe ta a matsayin ƴarsu.

Ba a jima da yin haka ba, Allah Ya ba su kyautar ƴan uku maza.

A wannan bidiyon, ta bayyana mana yadda ta tsinci kanta bayan yanke shawarar riƙon marainiyar da abubuwan da ta fuskanta kafin ta samu haihuwar ƴan ukunta.