Me maharan da ke satar ɗalibai a Najeriya ke son cimma?
Ku latsa hoton da ke ƙasa don kallon bidiyon:
Satar mutane don karɓar kuɗin fansa ta zama ruwan dare a wasu sassan Najeriya, amma a baya-bayan nan maharan sun mayar da akalar satar zuwa zuwa makarantun boko.
An sace fiye da ɗalibai 600 tun watan Disamban 2020 a wasu makarantu da kwalejin ilimi daban-daban a yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Me ke jawo sace-sacen ɗalibai a makarantun?