Yadda satar ɗalibai ke barazana ga makomar ilimi a arewacin Najeriya

Satar ɗalibai na neman zama ruwan dare musamman a arewacin Najeriya.

Daga watan Disamba, Ɗalibai da dama ne aka sace daga makarantu a arewa maso yammacin Najeriya, wanda ke nuna wani mummunan yanayi mai matukar tayar da hankali a matsalar satar mutane domin neman kuɗin fansa.

Ana kuma ganin matsalar satar ɗaliban babbar barazana ce ga ilimi a yankin arewacin Najeriya. Me ya sa ƴan bindiga ke kai hari makarantu da satar ɗalibai? BBC ta duba wannan batu.