Yemen: Yaro ɗan shekara 9 makaho da ke koyar da yara a yankin da ake yaƙi

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A yayin da ake gwabza yaƙi tsakanin gwamnati da ƴan tawayen Houthi a kusa da wata makaranta a birninTaiz, wani yaro ɗan shekara tara mai suna Ahmed ya kan koyar da yara a lokacin da ba malamai.

Yaron makaho ne tun haihuwarsa, kuma ya maye gurbin malamai wajen koyar da yaran a lokacin da malaman suka daina zuwa saboda rashin biyansu.

Duk makaranta ɗaya cikin biyar a Yemen an daina amfani da ita a cewar Asusun Kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, Unicef.

Amma a nan, ana ci gaba da koyarwa a makarantar duk da lalacewar da ta yi.