Matashin da ya yi amfani da kudin sayen IPhone don kasuwancin tsire a Kano

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani matashi a birnin Kano da ke Najeriya ya ce ya yi amfani da kudin da ya samu domin sayen wayar Iphone wajen soma sana'ar tsire.

Asim Balarabe Yazid ya ce wannan dabara ta zo masa ne bayan an sanya dokar kulle sakamakon cutar korona.

A cewarsa, yana koyarwa a makarantar gaba da sakandare da ke Abuja amma kullen da aka sa sanadin korona ya mayar da shi maras aikin yi.

Yazid ya ce yana samun alheri sosai a wannan sana'a kuma ba ya biyewa matasan da ke yi masa shagube.

Wasu bidiyon da za ku so ku kalla

Aism Balarabe Yazid ya ce wannan dabara ta zo masa ne bayan an sanya dokar kulle sakamakon cutar koroba.

A cewarsa, yana koyarwa a makarantar gaba da sakandare da ke Abuja amma kullen da aka sa sanadin korona ya mayar da shi maras aikin yi.

Yazid ya ce yana samun alheri sosai a wannan sana'a kuma ba ya biyewa matasan da ke yi masa shague.