Juyin juya hali a Masar: Shin kwalliya ta biya kudin sabulu?
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon:
Shekara 10 kenan tun bayan da Misrawa suka hau tituna don tunɓuke shugabansu da ya fi daɗewa a mulki, Hosni Mubarak.
Yunƙurinsu na daga wani ɓangare da juyin-juya hali a ƙasashen larabawa don kawo ƙarshen mulkin mulukiya.
Duk da cewa Mubarak ya sauka daga mulki, mutane da dama sun yi imani cewa, ba a cimma burin kasancewar Masar ƙasa mai bin tsarin dimokraɗiyya ba.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam suna zargin tsauraran takunkumai da aka ƙaƙaba kan ƴancin faɗin albarkacin baki ƙarƙashin shugaba mai ci Abdul Fattah al-Sisi. Amma hukumomi da masu goyon bayansa na cewa Sisi yana kare ƙasar ne daga shiga ruɗani.