...Daga Bakin Mai Ita tare da Umar M Sheriff
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Daga bakin mai ita wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.
A wannan kashi na 30, shirin ya tattauna da shaharraren mawaƙin fina-finai kuma tauraro wato Umar M Sherriff, inda ya ba mu labarin dalilin da ya sa ya fara waƙa.
A cikin hirar ya kuma amsa tambayoyi game da alaƙarsa da Abdul M Sheriff sannan ya gaya mana ko su waye manyan abokanansa a masana'antar.
Ɗaukar bidiyo: Yusuf Yakasai
Tacewa: Fatima Othman
Ga wasu na baya da za ku so ku kalla