Bidiyo: Cibiyoyin yi wa mutane bita kan zaman aure a Kano

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Mace-macen aure na daga cikin abin da ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya, musamman jihohi masu yawan al'umma irin Kano.

Duk da cewa babu wani adadi a hukumance da ke nuna yawan aurarrakin da ke mutuwa, amma an yi amanna yankin ne kan gaba a wannan matsala a Najeriya.

Wannan ce ta sa wasu suka fara buɗe cibiyoyin da za a dinga faɗakar da mutane maza da mata masu niyyar aure, sababbi da waɗanda ma suka taɓa yi kan zamantakewar auren da sauran abubuwa masu muhimmanci.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Kano kuma tsohon shugaban hukumar Hisbah, na daga cikin wadanda suka bugi ƙirji suka buɗe irin wannan cibiya.

Wasu bidiyo da za ku so ku kalla