Bidiyo: Me ya hana Buhari zuwa Kankara jajantawa iyayen ɗaliban da aka sace?
Ku latsa lasifikar da ke sama don kallon bidiyon:
A ranar Juma'ar da ta gabata da daddare ƴan bindiga suka dirarwa garin Ƙanƙara da ke jihar Katsina a arewa maso yammacin Najeriya inda suka yi awon gaba da ɗaliban makarantar sakandaren kimiyya ta maza su 333.
A wannan rana ce dai kuma gabanin satar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya tafi mahaifarsa Daura don yin hutu.
Duk da cewa yana Daura ɗin har yanzu, shugaban bai je ya jajantawa iyayen waɗannan yara ba, al'amarin da ya sa masu suka da masu sharhi suke ganin ba daidai ba ne, musamman ganin cewa duk cikin jiha ɗaya ne ba wata doguwar tafiya zai yi ba.