Recession: Hanyoyin da za ku bi don rage tasirin matsin tattalin arzikin da Najeriya ta shiga

Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda za ku rage tasirin matsin tattalin arzikin da Najeriya da shiga a kanku

Ku latsa hoton da sama don kallon bidiyon:

Masana tattalin arziki a Najeriya sun bayyana matakai da suke gani mutane marasa karfi za su bi domin rage tasirin da matsin tattalin arzikin da kasar ta fada a ciki zai yi a kansu.

A mako jiya ne hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta ce tattalin arziƙin Najeriya ya faɗi da kashi 3.62 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumba.

Hakan na nufin tattalin arziƙin ƙasar ya samu koma-baya mafi girma cikin shekara fiye da talatin.

Farfesa Nazifi Darma, masanin tattalin arziki a Jami'ar Abuja, ya shaida wa BBC cewa daya daga cikin hanyoyin ita ce mutane su rage yin abubuwan da ba su zama wajibi ba.

A cewarsa, ya zama wajibi matasa su rungumi sana'o'i su daina dogaro ga iyaye ko 'yan uwansu.